loading-texture
MURYOYIN DA BA A SAURARA BA
Waɗannan labarai na ɗauke ne da cikakkn bayani game da musgunawa da tashin hankali da cin zarafin da ya shafi sad
Domin kara fahimtar matsalar, sai kukunna sauti.
100%

MayakanBoko Haram sun kai farmaki a garinmu, wanda ya tilasta mu yin hijira. Na koma sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi tare da iyalina a shekarar 2016. Jim kaɗan bayan mun zauna a wannan wuri, sai tsohon mijina ya sanar da mahaifina cewa yana son ya sake aure na, (karo na biyu). Mahaifina kuwa ya aminta. Daga nan ya sake aurena. A lokacin ina ‘yar shekara 14.

https://www.safebirthevenhere.org/ha/unheardvoices/zainab

MayakanBoko Haram sun kai farmaki a garinmu, wanda ya tilasta mu yin hijira. Na koma sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi tare da iyalina a shekarar 2016. Jim kaɗan bayan mun zauna a wannan wuri, sai tsohon mijina ya sanar da mahaifina cewa yana son ya sake aure na, (karo na biyu). Mahaifina kuwa ya aminta. Daga nan ya sake aurena. A lokacin ina ‘yar shekara 14.

Yayin da nake tare da iyayena, ban kasance ina samun duk abin da nake so, duk da haka ina da ‘yanci.

Na yi da-na-sanin yin aure da wuri. Idan na ga ‘yan mata da ba su yi aure ba, nakan ji ɓacin rai. Amma nakan yi musu murnar cewa a ƙalla ba su da wani nauyi a kawunansu. Idan na kalli ‘ya’yana, nikan ji dama-dama, suna sa in ji farin ciki.

story-letter
*An canza sunan domin matsalar tsaro

Matada ke rayuwa a sansanonin‘yan gudun hijira sun kasance cibiyar da munanan aikin cin zarafin jinsin bil Adama kan fadawa.

A TSAWATA. A DAINA CIN ZARAFIN JINSI
WANDA YA ƊAUKI HOTUNA SHI NE: Etinosa Yvonne